14 Maris 2026 - 23:23
Source: ABNA24
Iran: Kasashen Da Mu Ke Makwabtaka Da Su Fitar dta Sojojin Amurka Daga Kasashensu

Araqchi: Iran na neman 'yan uwanmu makwabta da su kori sojojin 'yan kasashen waje daga yankinsu. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Araqchi; Laimar aminci da Amurka tai ta shelantawa a yanzu ya bayyana cewa cike ta ke da ramuka, Lemar da ba wai kawai ta iya kariya ba, sai dai a zahiri ta haifar da tashin hankali da rikici. 

Yanzu Amurka ya zame mata dole ta nema daga wasu, har ma daga China, da su taimaka wajen kiyaye da samar da aminci a mashigin Hormuz. 

Iran ta yi kira ga 'yan uwanta da ke makwabtaka da ita da su kori sojoji 'yan kasashen waje daga kasashensu; Musamman saboda kawai damuwa da abinda suka fi fifitaws shi ne kare Isra'ila. 

Araqchi: Za mu ci gaba da yakin kamar yadda ya dace don kada a sake maimaita wani yakin nan gaba. 

Ya kara da cewa: Ina kara tabbatar da cewa yaƙin da muke ciki ba mu muka fara shi ba Yaƙi ne da aka dora mana shi. 

Wannan Wani aiki ne na zalunci, rashin gaskiya, ba bisa ka'ida ba kuma ba tare da yunkurin yin saba. 

Muna kare kanmu ne kawai kuma za mu ci gaba da kare kanmu gwargwadon yadda ya cancanta ta yadda wannan yakin zai kawo karshe ba tare da sake faruwarsa a nan gaba ba.

Abin la'akari anan shi ne kamar yadda kafafen yaɗa ke tabbatar da cewa Yaƙi da Iran ya kai matsayin da ba za ku yi tsammanin sakamakonsa domin zai kutsa cikin sararin samaniyar kasuwanci hada-hadar kuɗi na duniya fiye da fagen fama na zahiri, kuma sun tabbatar da cewa iyakokin da aka saba da du na yaƙi ba su wanzuwa a wannan yakin.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha